By Mustapha Abdullahi Abubakar
Tsohon Shugaban ƙasar Nijeriya, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa, rashin shugabanci na gari shi ne babban abin da ke kawo cikas ga ci gaban ƙasashen Afirka.
Obasanjo ya bayyana cewa, idan aka samu shuwagabanni marasa kishi, ƙan Sashi kan rarrabu, ana sace dukiyar ƙasa, yara marasa ilimi suna karuwa wasu sukan kwana da yunwa, sannan matasa masu kyakkyawar makoma sukan yanke ƙauna tare da ɗaukar “mummunan fargaba” wajen neman abinci a ƙasashen waje.
Obasanjo ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a birnin Abeokuta, Jihar Ogun, yayin da yake jawabi ga ɗaliban da suka kammala karatu a Cibiyar Shugabanci ta Olusegun Obasanjo (OOLI).
An gudanar da taron yaye ɗaliban ne yayin taron bitar taya tsohon shugaban ƙasar murnar cikarsa shekaru 89 da haihuwa, mai taken “Wayar da kan Afirka na Duniya: Daga wani mataki zuwa Farfaɗowa.”
Taron, wanda aka gudanar a Olusegun Obasanjo Presidential Library da ke Abeokuta, ya samu halartar manyan mutane, da suka hada da tsofaffin ‘yan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyun LP, Peter Obi da na NNPP,Rabiu Kwankwaso; Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun; da tsoffin gwamnonin jihar, Sanata Ibikunle Amosun da Otunba Gbenga Daniel.
Recent:GOBARA TA ƘONE SHAGUNA A KASUWAR ABUBAKAR TATARI ALI DA KE AZARE.
