Daga Mustapha Abdullahi
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke wa Anamekwe Nwabuoku, tsohon mukaddashin Akanta Janar na tarayya, hukuncin daurin shekaru 72 a gidan yari bisa samunsa da laifin halasta kudaden haram kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito.
Karanta:FG to Scrap JSS Entrance Exams, Introduce Continuous Assessment System
Alkalin kotun, Mai shari’a James Omotosho, ya bayyana a yayin yanke hukuncin cewa Hukumar EFCC ta gabatar da hujjoji masu gamsarwa da suka tabbatar da laifin da ake tuhumar Nwabuoku da shi.
An same shi da laifin karkatar da kudade har Naira miliyan 868, lamarin da ya kai ga yanke masa wannan hukunci.
Recent:FG to Scrap JSS Entrance Exams, Introduce Continuous Assessment System
