Daga Mustapha Abdullahi
Ma’aikatar tsaron Qatar ta ce mutum shida sun mutu bayan wani jirgi mai saukar ungulu na ƙasar ya faɗo.
BBC ta ruwaito cewa Qatar ta ce jirgin ya rikito ne a lokacin da yake gudanar da atisayen da ya ”saba yi” bayan ya gamu da matsalar na’ura.
“Bayan ƙoƙarin nema, an samu nasarar gano gawarwakin mutum shida cikin bakwai da ke cikin jirgin,” kamar yadda ma’aikatar tsaron ƙasar ta bayyana a shafinta na X.
Karanta:ADC Moves To Reconcile Members After Court Ruling In Bauchi
Ma’aikatar ta ce cikin waɗanda suka mutu har da ƴan Turkiyya biyu fararen hula da sojan Turkiyyar ɗaya.
Game da wannan: A cikin makonnin baya-bayan nan Qatar na fuskantar hare-haren Iran. Kuma a wannan mako Iran ta kai hari kan babbar cibiyar adana gas ɗin Qatar. To amma ba a sani ba ko haɗarin wannan jirgi na da alƙa da yaƙin Iran ko a’a.
Recent:Rundunar ƴan sanda ta kama wani matashi da ake zargi da hallaka wani yaro
