Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da dakatar da barazanar kai hare-haren soji kan ƙasar Iran na tsawon kwanaki biyar.
A cewarsa, an ɗauki wannan mataki ne bayan wasu muhimman tattaunawa da aka gudanar tsakanin Amurka da Iran, da nufin lalubo mafita ga rikicin da ke ci gaba a yankin Gabas ta Tsakiya.
Karanta:Mutane 6 sun mutu sakamakon faduwar jirgi mai saukar ungulu a Qatar
Shugaban ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, inda ya ce ya umarci rundunar sojin Amurka da ta dakatar da duk wani shirin kai hari na wucin gadi.
A cewarsa, wannan dakatarwar za ta bai wa ƙoƙarin zaman lafiya damar ci gaba, tare da fatan rage tashin hankali a yankin.
Recent:FG to Scrap JSS Entrance Exams, Introduce Continuous Assessment System
