Daga Mustapha Abdullahi Abubakar
Aƙalla mutane 15 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka jikkata a hare-haren daban-daban da ‘yan bindiga suka kai a ƙauyukan Dansoda da Jikamshi da ke ƙananan hukumomin Dandume da Musawa a Jihar Katsina.
A cewar ‘yansanda da mazauna yankunan, hare-haren sun faru ne a yammacin ranar Talata.
Wani mazaunin Dansoda, Kabir Adamu, wanda ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a ranar Laraba, ya ce ‘yan bindigar sun kutsa cikin ƙauyen ne da misalin ƙarfe 8:00 na dare, inda suka kashe mutane 11 nan take.
A wani hari na daban kuma, an ruwaito cewa mutane huɗu sun mutu lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari a garin Jikamshi da ke ƙaramar hukumar Musawa.
Dukka wadanda suka rasa rayukansu, an riga an binne su bisa ga koyarwar addinin Musulunci.
