Dakarun rundunar Operation HADIN KAI sun dakile wani hari da mayaƙan ISWAP suka kai a sansaninsu da ke Goniri a ƙaramar hukumar Gujba ta jihar Yobe .
Mai magana da yawun rundunar, Sani Uba, ya ce harin ya faru ne tsakanin daren 9 zuwa safiyar 10 ga Maris, inda ‘yan ta’addan suka kai hari daga wurare da dama domin kewaye sansanin sojojin.
karanta:Ranar Mata ta Duniya: ‘Yan sanda sun bai wa zawarawan jami’an da suka rasu kayan abinci a Jigawa.
Ya bayyana cewa dakarun rundunar 120 Task Force Battalion tare da tallafin jiragen yaƙi sun yi gagarumar turjiya, lamarin da ya tilasta wa ‘yan ta’addan janyewa bayan sun yi asara mai yawa.
A cewarsa, an kashe fiye da ‘yan ta’adda 20, ciki har da wani babban kwamandansu mai suna Abu Yusu, yayin da sojoji suka kwato makamai da alburusai da dama.
Ya ƙara da cewa yankin na ci gaba da kasancewa a hannun sojoji, yayin da ake ci gaba da gudanar da sintiri da bincike domin kamo sauran ‘yan ta’addan da suka tsere.
Recent:Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 15, Sun Jikkata Da Dama A Katsina
