Kungiyoyin magoya baya sun sayi fom din takarar Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa ga Nentawe Yilwatda gabanin babban taron jam’iyyar na kasa da ke tafe.
Wasu kungiyoyin magoya bayan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun sayi fom din nuna sha’awa da na tsayawa takara domin goyon bayan Nentawe Yilwatda a matsayin dan takarar Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, gabanin babban taron jam’iyyar na kasa da ke shirin gudana.
An gabatar da fom din ne a hedikwatar jam’iyyar APC da ke Abuja ta hannun kungiyar Prince Simon Ali Support Organisation, wadda ta ce matakin na nuna irin goyon bayan da dan takarar ke samu a cikin jam’iyyar.
karanta:Fasinjoji da dama sun jikkata a hatsarin jirgin ƙasa na Abuja–Kaduna – NRC
Haka kuma, kungiyar Renewed Hope Women’s Network ta sayi fom din nuna sha’awa da na tsayawa takara ga Mary Alile-Idele.
Kungiyoyin sun bayyana cewa sayen fom din wani bangare ne na nuna karuwar goyon baya ga shugabancin jam’iyyar da kuma kudurin kara karfafa APC gabanin babban taron jam’iyyar na kasa.
Rahotanni sun nuna cewa ana sa ran babban taron na APC zai tattauna muhimman batutuwa da suka shafi makomar jam’iyyar da kuma zabin sabbin shugabanninta.
Zenith Media.
Recent:Ex-Rep Member Ahmed Abubakar “Garkuwan Misau” Dumps PDP for ADC
