Hukumar kula da jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC) ta tabbatar da cewa wasu fasinjoji sun jikkata bayan wani hatsari da ya auku da jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna da safiyar ranar Litinin.
Babban Daraktan hukumar, Kayode Opeifa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:30 na safe a kusa da tashar jirgin ƙasa ta Asham Train Station.
A cewarsa, hatsarin ya faru ne bayan injin jirgin da ke baya ya taɓa taragon fasinjojin da ke gabansa, sakamakon matsalar haɗin na’urar da ke ɗaure sassan jirgin.
Ya ƙara da cewa an garzaya da fasinjojin da suka samu raunuka zuwa cibiyoyin lafiya mafi kusa domin samun kulawar likitoci, tare da tabbatar da cewa babu wanda ya rasa ransa sakamakon hatsarin.
Karanta:Jam’iyyar APC na zawarcin gwamnan Bauchi Bala Muhammed, tare da masa tayin kujerar Sanata
A baya-bayan nan dai layin dogo a Najeriya, musamman wanda ke tsakanin Abuja da Kaduna, na fuskantar matsaloli na fita daga hanya. Wannan ya sa majalisar dattawa ta ƙaddamar da bincike kan matsalolin layukan dogo a shekarar 2025, karkashin jagorancin Adams Oshiomhole.
Zenith Media na ci gaba da bibiyar lamarin domin kawo muku karin bayani.
Recent:Tsohon Gwamnan Sakkwato, Wamako ya tallafa wa marayu 10,000 da Naira dubu ɗaya-ɗaya
