Daga Sani Adamu Hassan
Tsohon Gwamnan Sakkwato kuma Sanata mai wakiltar Sakkwato ta Arewa, Aliyu Magatakarda Wamako, ya bayar da tallafin Naira dubu dubu ga marayu 10,000 a faɗin jihar don gudanar da bikin karamar sallah cikin farin ciki da walwala.
Jaridar Daily Nigeria ta rawaito cewa Sanata Wamako ya miƙa tallafin ne ga hukumar Zakka ta jihar ta hannun shugaban hukumar Lawal Maidoki.
Recent:Jam’iyyar APC na zawarcin gwamnan Bauchi Bala Muhammed, tare da masa tayin kujerar Sanata
