Hukumar kula da Jos Main Market ta bayyana cewa gobarar da ta tashi a wani sashe na Terminus Market a daren Asabar 14 ga Maris, 2026, na iya samo asali ne daga tartsatsin wutar lantarki.
A cewar hukumar, rahotannin farko da suka samu sun nuna cewa ana zargin tartsatsin wutar lantarki daga ɗaya daga cikin shagunan da ke cikin yankin da abin ya shafa ne ya haddasa tashin gobarar.
Gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 10:00 na dare, inda jami’an tsaro tare da ma’aikatan Plateau State Fire Service da kuma Federal Fire Service suka garzaya wurin domin kashe wutar.
Karanta:ADC ta fitar da jadawalin zaɓen shugabannin jam’iyyar
Matakin gaggawar da jami’an kashe gobarar suka ɗauka ya taimaka wajen dakile yaɗuwar gobarar zuwa sauran sassan kasuwar, tare da rage yiwuwar asarar rayuka da dukiyoyi.
Hukumar kasuwar ta ce a halin yanzu ana ci gaba da tantance irin barnar da gobarar ta yi, yayin da bincike ke gudana domin tabbatar da ainihin musabbabin lamarin.
Hukumar ta kuma jaddada aniyarta na ci gaba da aiki tare da hukumomi da masu ruwa da tsaki domin ƙarfafa matakan tsaro a kasuwar, domin kauce wa sake faruwar irin wannan lamari a nan gaba.
– Zenith Media News
Recent:Idan ma Netanyahu bai mutu yanzu ba to nan gaba kaɗan za mu hallaka shi – Iran
