Ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi ta Muslim Rights Concern (MURIC) ta buƙaci gwamnatin tarayya ta tabbatar da samar da kashi 100 na ɗanyen mai ga matatun mai na cikin gida, musamman Dangote Refinery, domin ƙarfafa dogaro da kai a harkar makamashi a Najeriya.
A cikin wata sanarwa da Daraktan zartarwa na MURIC, Ishaq Akintola, ya fitar, ya yaba wa gwamnatin tarayya kan dakatar da shigo da fetur daga ƙasashen waje bayan ƙaruwa a samar da mai a cikin gida.
Sai dai ya ce abin damuwa ne yadda matatar Dangote mai ƙarfin tace ganga 650,000 a rana ke samun kusan kashi 28 zuwa 32 ne kawai na ɗanyen mai da take buƙata. Don haka ya buƙaci Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya fitar da umarnin shugaban ƙasa domin a rika bai wa matatun cikin gida cikakken ɗanyen mai.
Karanta:NSCDC ta kama tsohon shugaban ɗalibai bisa zargin satar kayan dakin gwaje-gwaje a Jigawa.
Har ila yau, MURIC ta yaba da shirin gwamnatin na raba kayan canza motoci daga fetur zuwa iskar gas (CNG) guda 100,000, tana mai cewa hakan zai taimaka rage tasirin tsadar man fetur ga al’umma.
A nata ɓangaren, shugaban Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority (NMDPRA), Saidu Mohammed, ya gargadi cewa bai kamata a koma zamanin dogaro da shigo da fetur daga waje ba, yana mai jaddada cewa dole ne a ci gaba da ƙarfafa tace mai a cikin gida.
Recent Nine Senators Defect to ADC
