Daga Mustapha Abdullahi
Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ce rikice-rikicen cikin gida da ke addabar yawancin jam’iyyun adawa alama ce ƙarara da ke nuna cewa ba su shirya karbar ragamar mulkin ƙasa ba.
Yilwatda ya bayyana haka ne a Abuja, yayin da yake jawabi kan muhimman batutuwan da suka shafi tafiyar da harkokin zamantakewa, siyasa da tattalin arziki a Najeriya.
Karanta:Atiku ga Tinubu: Raba shinkafa da taliya ba zai cece ka ba a zaɓen 2027
Ya ce duk wata jam’iyyar siyasa da ta kasa tafiyar da al’amuranta na cikin gida, ko kuma ta gaza sasanta saɓanin ra’ayi, tabbatar da ɗa’a, da gina haɗin kai a cikinta, ba za a iya ɗora mata nauyin tafiyar da ƙasa mai sarkakiya kamar Najeriya ba.
Shugaban APC na ƙasa ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su kasance masu fahimta da hangen nesa, domin su iya bambance tsakanin
hayaniya da nagartar aiki, fargaba da shiri na gaskiya, son kai na siyasa da sahihin shugabanci.
Recent:Nijar da Turkiyya sun kulla yarjejeniyar horon Sojoji
