Daga Mustapha Abdullahi Abubakar
Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya kaddamar da aikin gina sabbin makarantu 102 da kuma gyaran makarantu da cibiyoyin ilimi 170 a dukkanin kananan hukumomi 23 na jihar karkashin shirin (ROOSC).
Gwamnan ya ce wannan shiri na daga cikin matakan da gwamnatinsa ke dauka domin fadada damar samun ingantaccen ilimi da kuma rage yawan yaran da ba su zuwa makaranta a jihar.
Da yake jawabi yayin bikin kaddamar da aikin a ranar Laraba, Mista Sani ya bayyana cewa shirin wata babbar alama ce ta kudurin gwamnatin jihar na tabbatar da cewa kowane yaro a Kaduna ya samu damar yin karatu da cimma burinsa.
Karanta:MAJALISAR KANO TA ƘADDAMAR DA MATAKAN TSIGE MATAIMAKIN GWAMNA AMINU GWARZO
Ya ce shirin ba wai kawai fara aikin gine-gine ba ne, illa kuma wata alama ce ta jajircewar gwamnati wajen daukar ilimi a matsayin ginshikin ci gaban al’umma.
Gwamnan ya bayyana cewa tun bayan hawansa mulki a 29 ga Mayu, 2023, gwamnatinsa ta mayar da hankali
Recant:DANGOTE REFINERY TA CE ZA TA WADATA NAJERIYA DA ISASSHEN MAN FETUR
