Daga Sani Adamu Hassan
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya halarci sauya sheƙar ‘yan majalisar tarayya takwas daga jam’iyyar NNPP zuwa APC a Majalisar Dokoki ta Ƙasa da ke Abuja.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sanusi Dawakin-Tofa, ya fitar a Kano ranar Laraba.
Sanarwar ta ce ‘yan majalisar sun bayyana rikicin cikin gida da ke addabar NNPP a matsayin dalilin sauya sheƙar tasu.
Ƴan majalisar da suka sauya sheƙar sun haɗa da Tijjani Abdulkadir Jobe, Garba Ibrahim Diso, Hassan Shehu Hussain, Idris Dankawu, Muhammad Chiroma Nalaraba, Rabiu Yusuf, Dr. Ghali Mustapha Tijjani da kuma Muhammad Bello Shehu.
karanta:SHUGABAN ƘARAMAR HUKUMAR MANGU YA SAKA DOKAR HANA FITA A CIKIN GARIN MANGU.
Sanarwar ta ambato Gwamna Yusuf na cewa wannan ci gaban wani bangare ne na tsarin dimokuradiyya, yana mai jaddada cewa sauya sheƙar ‘yan siyasa ba sabon abu ba ne a cikin ingantacciyar dimokuradiyya.
Hakazalika, ya sake tabbatar da kudurin gwamnatinsa na ci gaba da kai wa al’ummar Jihar Kano ribar dimokuradiyya, ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba.
Sanarwar ta kuma jaddada bukatar hadin kai da hadin gwiwa tsakanin zababbun wakilai domin bunƙasa ci gaban jihar gaba ɗaya.
Recent:Kotu ta soke umarnin sammacin kama Kabiru Turaki a Abuja
