Daga Mustapha Abdullahi
Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta soke umarnin sammacin kama shugaban tsagin jam’iyyar PDP, Kabiru Turaki, wanda ta bayar a ranar 26 ga watan Maris, 2026.
Mai shari’a Peter Kekemeke ne ya soke sammacin a yau Laraba, bayan lauyan Turaki, Chris Uche (SAN), ya gabatar da bukatar baki a gaban kotu, sakamakon bayyanar wanda ake kara a zaman kotun.
Da aka fara sauraron karar, Uche ya nemi afuwar kotu bisa rashin halartarsa a zaman da ya gabata, yana mai bayyana cewa yana wajen kasar ne a lokacin, kuma ya dawo ne a safiyar ranar Laraba kafin ya wuce kai tsaye zuwa kotun.
Haka kuma, ya nemi afuwa a madadin Turaki, yana mai cewa shi babban lauya ne (SAN) kuma mutum ne mai girmama kotu. Ya kara da cewa rashin halartar Turaki a zaman da ya gabata ba da gangan ba ne, kuma bai taba nufin raina kotu ba.
Karanta:Nijeriya ba za ta miƙa wuya ga ’yan ta’adda ba – Gwamnatin Tarayya
A nasa bangaren, lauyan masu gabatar da kara, Usman Rabiu, ya bayyana cewa ba su da wata adawa da bukatar da aka gabatar. Ya ce manufar bayar da sammacin kama Turaki ita ce tabbatar da ya gurfana a gaban kotu, wanda kuma hakan ya cika da zarar ya halarta.
A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Kekemeke ya lura cewa Turaki ya bayyana a gaban kotu da kansa kafin a aiwatar da sammacin kama shi. Don haka, kotun ta yanke shawarar yafewa wanda ake kara tare da soke sammacin kama shi.
Recent:SHUGABAN ƘARAMAR HUKUMAR MANGU YA SAKA DOKAR HANA FITA A CIKIN GARIN MANGU.
