By Mustapha Abdullahi Abubakar
Wata gobara ta auku a daren Alhamis, 5 ga watan Maris 2026, a cikin Kasuwar Abubakar Tatari Abubakar Tatari Ali da ke garin Azare a Jihar Bauchi.
Rahotanni daga shaidun gani da ido sun bayyana cewa gobarar ta tashi ne a wani ɓangare na layin masu sayar da yadudduka, inda wutar ta bazu ta lalata shaguna da dama.

Jami’an kwana-kwana tare da masu aikin agaji sun garzaya wurin domin kashe wutar da kuma dakile yaduwarta zuwa sauran sassan kasuwar.
Karanta:ISWAP Sun Hallaka Sojoji 14 A Borno
Har yanzu dai ba a tabbatar da cikakken adadin shagunan da suka lalace sakamakon gobarar ba, yayin da ake ci gaba da tattara bayanai kan lamarin.
