By mustapha Abdullahi Abubakar
Dakarun Rundunar Soji ta Uku ta Najeriya (3 Division Nigerian Army) sun samu nasarar ƙwato ƙauyen Mansur da ƙauyukan da ke kewaye da shi a ƙaramar hukumar Alkaleri, Jihar Bauchi, a wani ɓangare na ci gaba da gudanar da Aikin Operation BUGUN KARKANDA III.
Aikin, wanda Manjo Janar Folusho Oyinlola, Babban Kwamandan Rundunar Soji ta Uku kuma Kwamandan Operation ENDURING PEACE, ke jagoranta, yana mayar da hankali ne kan ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka da ke addabar al’ummomin yankin.
Majiyoyin soji sun bayyana cewa dakarun sun kai hari na haɗin gwiwa a wuraren da aka gano ‘yan ta’addan suna fakewa, inda suka fatattake su bayan sun yi yunƙurin kwace ikon ƙauyen Mansur. Haka kuma, an kwato bindigar AK-47 guda ɗaya yayin aikin bincike da tsabtace yankin, wanda hakan ya rage ƙarfin ayyukan ‘yan ta’addan a yankin.
Matakin na nuna jajircewar rundunar soji wajen tabbata
