Matatar mai ta Dangote Refinery, wadda ita ce mafi girma a nahiyar Afirka, ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da samar da isasshen man fetur domin biyan bukatun ƴan Najeriya.
Kamfanin ya bayyana hakan ne bayan ɓarkewar rikicin da ke ƙara kamari a yankin Gabas ta Tsakiya, wanda ya janyo tashin farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya, lamarin da ya haddasa fargaba kan yiwuwar ƙarancin man fetur a wasu ƙasashe.
Karanta:MAJALISAR KANO TA ƘADDAMAR DA MATAKAN TSIGE MATAIMAKIN GWAMNA AMINU GWARZO
Dangote Refinery ta ce duk da irin wannan yanayi da ake ciki a kasuwar mai ta duniya, matatar na da ƙarfin samar da wadataccen man fetur da zai rika wadatar da kasuwar Najeriya, tare da rage dogaro da shigo da mai daga ƙasashen waje.
Masu kula da matatar sun jaddada cewa za su ci gaba da aiki tukuru domin tabbatar da cewa ƴan Najeriya ba su fuskanci matsalar ƙarancin man fetur ba, musamman a wannan lokaci da ake fama da sauye-sauyen farashi a kasuwar duniya.
Zenith Media ta ruwaito cewa wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin da ake yi na ƙarfafa samar da mai a cikin gida da kuma tabbatar da wadatarsa ga al’umma.
Recent:Majalisar Dattawa Ta Gayyaci Tsohon Shugaban NNPCL, Mele Kyari, Kan Zargin Naira Tiriliyan 210
