Ƴansanda sun kama wani mutum bisa zargin yin lalata da ɗan ƙaramin yaro a Bauchi
Daga Mustapha Abdullahi
Rundunar ƴansanda ta Jihar Bauchi ta kama wani mutum mai shekaru 48, Bala Mato, bisa zargin yin lalata da wani yaro mai shekaru 15 a garin Burra, ƙaramar hukumar Ningi.
An kai rahoton lamarin ne a ranar 25 ga watan Fabrairu, 2026, ta bakin Danalami Umar, wani mazaunin Bakin Kasuwa, Burra.
Karanta:Akwai yiyuwar mutum 2 sun rasa rayukansu a rikicin kabilanci a jihar Adamawa
‘Yansanda sun ce an yi zargin cewa wanda ake zargi ya ja ƙaramin yaron zuwa ɗaki a ranar 17 ga watan Fabrairu, da misalin ƙarfe 8 na dare, inda aka aikata laifin.
A cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin Facebook na rundunar a ranar Lahadi, SP Nafiu Habib, jami’in hulda da jama’a na ‘yansanda, ya ce an kama wanda ake zargin, kuma an kai wanda abin ya shafa Asibitin Gwamnati, Burra, don gwajin lafiya.
Recent:Gwamnatin Plateau Ta Naɗa Kwamitin Rabon Tallafin Ramadan da Sallah 2026
