Daga Mustapha Abdullahi Abubakar
Majalisar dokokin Habasha ta bada hutun kwanaki uku don gudanar da zaman makoki a ƙasar, dai-dai lokacin da adaɗin waɗanda suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa da zabtarewar ƙasa da aka samu a kudancin yankin Gamo ya kai 80, inda ke ci gaba da neman waɗanda suka ɓace.
A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook, majalisar ta ce za a fara zaman makokin na kwanaki uku ne daga yau Asabar, don ƙarrama waɗanda suka rasa rayukansu.
Ta ce kawo yanzu an tabbatar da mutuwar mutane 80 a sanadiyar iftila’il, adadin da ƴansanda suka ce ka iya ƙaruwa, sannan ana ci gaba da neman waɗanda suka ɓace.
Karanta:Jami’an tsaron Najeriya da dama ne suka mutu a wani hari da aka kai jihar Filato.
Tun da farko shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, wanda ɗan asalin ƙasar ne ta Habasha ne, ya sanar da cewar dubban mutane ne suka rasa matsugunansu sakamakon iftila’in.
WHO ta samar da tawagar bada agajin gaggawa da ta tura don taimakawa waɗanda abin ya shafa, musamman a ɓangaren kiwon lafiya.
Recent:Jami’an tsaron Najeriya da dama ne suka mutu a wani hari da aka kai jihar Filato.
