Daga Mustapha Abdullahi Abubakar
Aƙalla sojojin Najeriya da ƴan banga 20 ne suka mutu, a lokacin da wasu ƴan ta’adda ɗauke da muggan makamai suka yi wa tawagarsu da ke gudanar da sintiri kwanton ɓauna, a yankin Garga da ke ƙaramar hukumar Kanam a jihar Filato.
Jaridar Vanguard da ke wallafawa a Najeriya ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 4 na yammacin jiya Juma’a, inda tawagar sojoji da ƴan banga da ke sintiri a garuruwan Garga da Kyaram da Gyambau, da sauran garuruwan yankin ne ƴan ta’addan suka yi kai wa hari a kusa da Wanka.
A cewar sanarwar da ƙungiyar ci gaban al’ummar Kanam ta fitar a yau, ta ce kimanin jami’an soji 12 da suka haɗa da manyan hafsoshin soji biyu ne suka rasa rayukansu a wannan hari, yayin da ƴan banga takwas suka rasa rayukansu.
Karanta:Sojoji sun kama wanda ake zargi da kai hari a wata al’umma a Jihar Benue.
Sanarwar wacce ta samu sahannun shugaban ƙungiyar Barr. Garba Aliyu da sakatarenta Shehu Kanam, ta ce an kuma samu rahoton kashe wasu ƴan ta’adda a yayin musayar wutar da suka yi da jami’an tsaro.
Bayanai sun ce bayan wancan artabu, maharan sun afkawa garin Kyaram, inda suka yi awon gaba da kayayyaki da shanu masu yawan gaske daga mazauna yankin.
Ƙungiyar ta Kanam ta bayyana harin a matsayin wani ɓangare na matsalar tsaro da ta daɗe tana addabar al’ummomin kan iyakar jihohin Filato da Taraba da kuma Bauchi.
Recent:Tsangaya association seeks Bauchi govt recognition after court rulings
