Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa fom na neman tsayawa takarar gwamna a jam’iyyar APC gabanin zaɓen 2027.
Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Dawakin-Tofa, ya bayyana cewa gwamnan ya miƙa fom din ne tare da rakiyar tsohon gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau; Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin; Sanata Kawu Sumaila da sauran manyan jiga-jigan siyasa daga Kano.
Bayan miƙa takardun, gwamnan ya ce neman wa’adi na biyu wata sabuwar dama ce ta ci gaba da yi wa al’ummar Kano hidima.
Karanta:Gwamnatin Oyo ta hana sayar da raguna a manyan tituna lokacin babbar Sallah
Ya yi alƙawarin faɗaɗa ayyukan inganta birane, gina hanyoyi, magudanan ruwa da gyaran kasuwanni, tare da ƙara mayar da hankali kan bunƙasa yankunan karkara ta hanyar samar da hanyoyi, ruwa, makarantu da cibiyoyin lafiya.
Haka kuma ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa manoma da matasa domin samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arziki.
Gwamnan ya sake jaddada aniyarsa ta inganta ilimi da harkokin lafiya tare da tabbatar da haɗin kai da zaman lafiya a jihar.
Idan za a iya tunawa cewa Abba Kabir Yusuf ya sauya sheƙa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC a watan Janairun 2026 bayan rikice-rikicen cikin gida a jam’iyyarsa ta baya.
Recent:Masu neman takarar gwamnan Yobe a APC sun yi watsi da tsayar da ɗan takara ta maslaha
