Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa, ya amince da ɗaukar sabbin malaman makaranta 2,158 domin cike guraben da ake da su a makarantun gwamnati a faɗin jihar.
Sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar ta bayyana cewa, daga cikin adadin da za’a ɗauka, malamai 1,500 za’a tura su makarantun firamare; yayin da 658 za su koyar a makarantun sakandare.
karanta:Gwamna Yusuf ya shaida sauya sheƙar ‘yan majalisar tarayya 8 daga NNPP zuwa APC a majalisar taraiya
Gwamnatin ta ce matakin na daga cikin ƙoƙarin inganta harkar ilimi a jihar, musamman wajen rage giɓin adadin malamai da ɗalibai da kuma ƙarfafa ingancin koyarwa a matakin firamare da sakandare.
Kwamitin da gwamnati ta kafa domin gudanar da aikin ɗaukar malaman ya buɗe ƙofar karɓar aikace-aikace daga ƴan asalin jihar da suka cika ƙa’idojin da ake buƙata, domin cike guraben da aka tantance a wasu makarantu bisa la’akari da darussan da ake buƙata.
Recent:MURIC Ta Zargi Caleb Mutfwang Da Nuna Wariya Ga Musulmai
