Daga Mustapha Abdullahi Abubakar
Mazauna kauyen Mai Tukunya da ke yankin Dansadau, a ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara, sun fara tserewa daga gidajensu bayan da ’yan bindiga suka ba su wa’adin ƙarshe, inda suka bukaci a ba su naira miliyan 10, bindigar AK-47 guda ɗaya, da baburan Honda uku, a matsayin sharadin da zai ba su damar ci gaba da zama a ƙauyen.
Rahotanni sun bayyana cewa iyalai gaba ɗaya, ciki har da yara da tsofaffi, sun fara barin gidajensu suna tafiya cikin zafin rana ba tare da sanin inda za su nufa ba.
A cewar wani masani kan harkokin tsaro mai suna Bakatsine, wani mazaunin yankin ya bayyana irin tasirin wannan buƙata ga iyalan da suka shafe fiye da shekaru goma suna rayuwa cikin barazana.
Dukiyar da mutane suka taɓa mallaka ta lalace sannu a hankali, ta bar su cikin yunwa, tsoro da rashin tabbas.”
Wannan mazaunin ya kuma bayyana irin haɗarin da al’ummar ke fuskanta kullum kafin a ba su wannan wa’adi.
“Rayuwa a cikin al’ummar ta zama kamar caca da mutuwa a kullum.
A kowane lokaci, masu ɗauke da makamai kan kai farmaki gidaje, suna cin zarafin mata da ’yan mata,” in ji rahoton.
“Maƙiyaya da manoma kan fuskanci haɗarin kashewa ko sacewa idan suka fita kasuwa ko gonaki. Iyaye kan tura ’ya’yansu makaranta cikin tsoron cewa watakila ba za su dawo ba.”
Mazauna yankin sun ce a wasu lokuta ana ba su shawarar su kare kansu, duk da cewa ba su da makamai ko horon da zai ba su damar tunkarar ’yan bindiga masu muggan makamai.
Rahoton ya ce, da yake babu wata mafita mai kyau da ta rage musu, mutanen ƙauyen sun zaɓi ceton rayuwarsu maimakon nacewa a ƙasar da suke zaune. Iyalai gaba ɗaya — yara, mata, tsofaffi da masu rauni — sun fara wata tafiya mai raɗaɗi ta gudun hijira.
Rahotanni sun nuna cewa iyalai da dama sun yi tafiya na sa’o’i a ƙafa, wasu ma suna cikin azumin watan Ramadan.
karanta:NSCDC ta kama tsohon shugaban ɗalibai bisa zargin satar kayan dakin gwaje-gwaje a Jigawa.
Waɗanda suka rage a ƙauyen kuma na fuskantar barazanar rasa rayukansu.
Masanin tsaron ya bayyana cewa halin da Mai Tukunya ke ciki yana nuna irin matsalar tsaro da ta mamaye yankin gaba ɗaya.
Ya ce:“Labarinsu yana nuna wata babbar matsalar ƙasa baki ɗaya. A yankin, rashin tsaro ya sa hanyoyi ba su da aminci, gidaje ba su da tabbaci, makarantu kuma suna fuskantar hare-hare da garkuwa da mutane. Al’ummomin da a da suke bunƙasa yanzu suna watsewa yayin da tsoro ke maye gurbin fata.”
Recent:MURIC ta buƙaci NNPC da ya riƙa baiwa matatar man Dangote isasshen ɗanyen mai
