Daga Mustapha Abdullahi Abubakar
A wani bangare na kokarin karfafa ingancin ayyukan tsaro da kuma bunkasa tsaron da ya fi mayar da hankali ga jama’a a cikin rundunar, Hukumar Tsaro da Kariya ta Farar Hula ta Najeriya (NSCDC) ta fara wani taron horaswa na kwanaki biyu kan yadda za a hada ka’idojin tsaron dan Adam cikin ayyukan rundunar.
Taron na gudana ne a Dakin taro na Dr. Ade Abolurin da ke hedikwatar NSCDC a baban birni tarayya , Abuja.

Wannan shiri ya yi daidai da hangen nesan Babban Kwamandan rundunar (Commandant General) Ahmed Abubakar Audi, mni, OFR, na gina rundunar tsaro mai ladabi, mai amfani da bayanan sirri, kuma mai mayar da hankali ga kare jama’a.
Taron an shirya shi ne domin bai wa jami’an rundunar ilimi da kwarewa kan yadda za su hada ka’idojin tsaron dan Adam cikin shirye-shiryen aiki da kuma ayyukan da suke yi a filin aiki.
An bude taron ne a madadin Babban Kwamandan rundunar ta hannun Mukaddashin Mataimakin Babban Kwamanda mai kula da horaswa da bunkasa ma’aikata, ACG Mukhtar Lawal, mni.
Karanta:KASAR IRAN BAZASU BUGA GASAN CIN KOFIN DUNIYA BA.
Wannan shirin bunkasa kwarewa yana samun goyon baya daga Ofishin Harkokin Waje, Commonwealth da Raya Kasa (FCDO) da kuma Cibiyar Kare Fararen Hula a Rikice-rikice (Center for Civilians in Conflict). Hakan na nuna hadin gwiwar da aka kulla domin karfafa kariyar fararen hula, musamman yara da sauran mutane masu rauni da rikice-rikice da rashin tsaro ke shafa.
Babban Kwamandan rundunar ya sake jaddada cewa hada ka’idojin tsaron dan Adam cikin ayyukan rundunar yana daga cikin manyan matakan da za su taimaka wajen sake inganta rundunar domin kare manyan kadarorin kasa da muhimman gine-gine, da kuma karfafa tsarin tsaro na al’umma tare da tabbatar da ayyukan tsaro masu kwarewa da mayar da hankali ga jama’a a fadin kasar nafadinR
