Daga Mustapha Abdullahi
Aƙalla mutane 56, galibinsu ’yan kasuwa, ake fargabar sun rasa rayukansu yayin da wasu 14 suka jikkata sakamakon wani harin sama da aka kai a wata kasuwa ta mako-mako da ke kan iyakar jihohin Borno da Yobe.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a kasuwar Jilli, wadda ke tsakanin ƙananan hukumomin Gubio a Jihar Borno da Geidam a Jihar Yobe, a ranar Asabar.
Rahotanni sun nuna cewa an kai harin ne a yayin wani samame na sojoji da ke farautar ’yan ta’addan Boko Haram. Sai dai an ce harin ya kauce daga inda aka nufa, ya afkawa jama’ar da ke gudanar da harkokinsu a kasuwar.
Karanta:Gwamna Dauda Lawal ya jajanta wa waɗanda harin ‘yan bindiga ya rutsa da su a Bukkuyum
Kasuwar Jilli na jawo ’yan kasuwa da masu saye daga yankuna da dama, ciki har da Gubio, Chiweram da Benisheikh a Borno, da kuma Gurokayeya da Geidam a Yobe.
Wasu majiyoyi sun ce jirgin yaƙi da ya kai harin na bin diddigin wasu da ake zargi ’yan tada ƙayar baya ne da suka je kasuwar domin karɓar haraji daga hannun ’yan kasuwa da kuma samun kayan abinci. Amma harin ya kasa cimma manufarsa.
Wani ganau ya bayyana cewa akalla gawarwaki 56 aka tabbatar, yayin da wasu mutum 14 ke karɓar magani a Asibitin Kwararru da ke Geidam a Jihar Yobe.
Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, rundunar sojin saman Nijeriya ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance dangane da lamarin ba.
Recent:Kamfanin NNPC ya samu Naira Tiriliyan 2.68 kuɗin shiga duk da raguwar man da ake hakowa
