Daga Sani Adamu Hassan
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi ta tabbatar da cafke wani matashi da ake zargi da hannu a sace wani ƙaramin yaro mai shekaru huɗu da kuma kashe shi a cikin garin Bauchi.
A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Nafiu Habib ya fitar, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan wani mazaunin unguwar Nasarawa Madina Quarters a cikin garin Bauchi, Salisu Yunusa, ya kai rahoto a ranar 21 ga watan Maris da misalin ƙarfe 11 na safe cewa dansa Yunusa Salisu ya ɓace tun ranar 18 ga watan Maris da misalin ƙarfe 9:30 na safe.

Mahaifin yaron ya kuma bayyana cewa ya samu kira daga wata boyayyiyar lamba a ranar 19 ga watan Maris inda aka nemi kudin fansa na naira dubu dari biyar (₦500,000), kuma ya biya naira dubu dari (₦100,000) ba tare da ganin dansa ba.
Binciken da ‘yan sanda suka gudanar ya kai ga cafke wani matashi mai suna Rabiu Safiyanu mai shekaru 20, wanda ke zaune a unguwar, kuma abokin ƙanin mai ƙarar ne wato mahaifin yaron da aka sace, wanda hakan ya ba shi damar shiga gidan ba tare da wani shakku ba.

Albarka Radio ta rawaito cewa wanda ake zargin ya amsa laifinsa inda ya bayyana cewa shi ne ya sace yaron, ya shake shi har lahira, sannan ya jefar da gawarsa a Dutsen Warinje, tare da ci gaba da neman karin kudin fansa.
karanta:Group Empowers Bauchi Youths On Electoral Reforms, Political Participation
‘Yan sanda sun ce sun gano gawar yaron wacce ta fara lalacewa, tare da alamun an shake shi da igiya, inda jami’in asibitin ‘yan sanda ya tabbatar da rasuwarsa.
Daga bisani aka dauki hotunan gawar kafin a mika ta ga iyalansa domin yi masa jana’iza cikin gaggawa saboda lafiyar jama’a.
A halin yanzu, wanda ake zargin yana tsare a hannun ‘yan sanda, yayin da kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Sani-Omolori Aliyu, ya umarci sashin binciken manyan laifuka da su karɓi lamarin domin zurfafa bincike tare da tabbatar da an gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.
Recent:ADC Moves To Reconcile Members After Court Ruling In Bauchi
