Daga Mustapha Abdullahi Abubakar
Wasu bayanai da ke fitowa daga Gabas ta tsakiya na cewa ƙasashen Pakistan, Turkiyya da Masar na shiga tsakani a tattaunawar da shugaban Amurka Donald Trump ke cewa yana yi da wani babban jagora a Iran duk da bai bayyana ko wanene ba.
Duk da cewa babu tabbaci game da shiga tsakanin waɗannan ƙasashe, amma majiyoyi masu ƙarfi na nuna cewa waɗannan ƙasashe ne ke taka muhimmiyar rawa don ganin an kawo ƙarshen wannan yaƙi da Trump ya sha alwashin dakatar da shi da zarar an kafa sabuwar gwamnati a Iran.
Wasu bayanai daga masu sanya idanu da kuma sharhi kan kalaman na Trump sun nuna cewa akwai yiwuwar cewa ana tattaunawa ne da ministan harkokin wajen ƙasar Abbas Aragchi, duk da babu sanarwa game da haka a hukumance.
KARANTA:Kotu ta yanke wa tsohon akanta janar hukuncin daurin shekaru 72 kan badakalar N868m
Turkiyya na cikin ƙasashen da ke taka muhimmiyar rawa wajen shiga tsakani a rikice-rikicen da ke faruwa a duniya, dalili kenan da ya sanya ake ganin wataƙila tana da rawar da zata iya takawa a tsayar da wannan rikici.
Rufe mashigin Hormuz da Iran ta yi da kuma barazanar dasa nakiyoyin ƙarƙashin teku da nufin tarwatsa duk jirgin ruwan da yayi yunƙurin wucewa ta wajen ya yiwa ƙasashe da dama illa ta fuskar tattalin arziki, wataƙila dalili kenan da ya tilasta neman wannan zama da Iran wanda babu tabbas a cikinsa.
