Daga Mustapha Abdullahi
Jariran, waɗanda aka ƙiyasta sun kai kimanin watanni biyar kuma aka gano mace da namiji ne, an ce, an same su ne a cikin leda…
Mazauna yankin “Special Site” da ke Karamar Hukumar Pankshin a Jihar Filato sun bayyana alhini da ɓacin rai bayan gano wasu jarirai tagwaye a cikin bola a yankin.
Gano jariran, wanda ya faru a ranar Laraba, ya bar mazauna yankin cikin damuwa, inda wasu suka bayyana lamarin a matsayin abin ban tausayi da kuma ban tsoro.
Jariran, waɗanda aka ƙiyasta sun kai kimanin watanni biyar kuma aka gano mace da namiji ne, an ce, an same su ne a cikin leda a wani wurin zubar da shara da ke bayan gidajen mutane.
Wani mazaunin yankin mai suna Enman Danladi, wanda gidansa yake kusa da bolar, ya bayyana yadda aka gano su:
Ni direban tasi ne mai zirga-zirga a cikin gari. Lokacin da na dawo daga aiki, sai wani mutum da yake noman rani a bayan gidana ya zo ya sanar da ni abin da ya gani,” kamar yadda ya bayyanawa Daily Trust.
Karanta:Sanitation Exercise to Hold Low-Key in Plateau Over UTME Mock
“Ya ce ya lura da wani kare yana shinshina wata leda, yayin da ƙudaje ke ta yawo a kanta. Wannan ya ba shi masaniya. Bayan ya kora karen, sai ya duba ledar ya ga ashe tagwaye ne, sannan ya rugo da gudu ya faɗa mini.”
A cewarsa, nan take ya sanar da sauran mazauna yankin, inda mutane kusan takwas suka taru a wurin. “Dukanmu mun je can kuma mun tabbatar da abin da ya gani. Gaskiya abin ya tayar mana da hankali sosai,” in ji shi.
