Gwamnatin Jihar Plateau ta sanar da cewa za a gudanar da aikin tsabtace muhalli na wata-wata da aka saba yi a ranar Asabar, 28 ga Maris, 2026, cikin sauƙi.

An dauki wannan mataki ne domin bai wa ɗalibai da jami’an da za su halarci jarabawar gwaji ta UTME (Mock), wadda za ta fara da ƙarfe 6:00 na safe a ranar, damar motsi ba tare da wata tangarda ba.
Daraktan Janar na Hukumar Kula da Muhalli da Tsabtace Jihar Plateau (PEPSA),

Samuel Nathaniel Dapiya, ya ce duk da haka ana sa ran mazauna jihar za su tsaftace muhallinsu tare da bin ƙa’idojin tsafta.
Karanta:Eh, na taɓa zamowa ɗan fashi da makami kafin Yesu ya kira ni” – inji Rev.Dachomo
Hukumar ta roƙi al’umma da su bayar da haɗin kai da fahimta, tare da jaddada muhimmancin kiyaye tsafta domin tabbatar da muhalli mai kyau da lafiya a fadin jihar.
Recent:One-Party System Dangerous As Parties Face Crisis In Nigeria, Bauchi –Says Abubakar Kari
