Daga Mustapha Abdullahi
Ƙungiyar kafafen yada labarai na radiyo da talabijin ta karrama Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal da lambar yabo ta “Gwamnan Shekara a Fannin Gine-gine” sakamakon ayyukan raya birane da ya gudanar a jihar.
Daga cikin ayyukan da suka ja hankali aka ba shi wannan lambar yabo akwai gina filin jirgin sama na zamani, gyaran asibitoci, da kuma gina da gyara makarantu sama da 800 a ƙananan hukumomi 14 na jihar.
karanta:Jam’iyyun adawa ba su shirya karɓar mulki a hannun APC ba – Yilwatda
Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar ta ce an ba shi lambar yabon ne a taron BON karo na biyu da aka gudanar a Abuja.
Ƙungiyar ta yaba da irin sauye-sauyen da gwamnatin Lawal ta kawo musamman wajen raya birnin Gusau da sauran ayyukan more rayuwa a faɗin jihar.
