Daga Mustapha Abdullahi
Shugabar ƙasar Tanzania, Samia Suluhu Hassan, ta umarci jami’an gwamnati da su riƙa amfani da motar bas wajen tafiye-tafiyen aiki domin rage yawan amfani da man fetur, sakamakon ƙarancin da da ya biyo bayan rikicin Gabas ta Tsakiya.
A cewar hukumomin kula da makamashi a ƙasar, farashin mai ya ƙaru da kusan kashi ɗaya bisa uku tun watan Maris.
Da ta ke jawabi yayin bikin rantsar da wasu jami’ai a ranar Laraba, Samia ta ce a duk lokacin da za ta yi tafiyar aiki, motocin rakiyarta za su takaita ne ga muhimman motocin tsaro kaɗai, kamar motocin jami’an tsaro, ‘yan sanda, da motar taimakon gaggawa.
karanta:Nijar da Turkiyya sun kulla yarjejeniyar horon Sojoji
A baya, ayarin motocin shugabar kan kai fiye da motoci 30, ciki har da manyan motocin alfarma da ‘yan sandan rakiyar hanya, lamarin da kan jawo cunkoson ababen hawa.
Rahotanni sun ce matsalar ta samo asali ne daga tasirin rikicin Gabas ta Tsakiya, musamman bayan Iran ta hana zirga-zirga yadda ya kamata a mashigar Hormuz, wata muhimmiyar hanya da kusan kashi 20 cikin 100 na man fetur da iskar gas na duniya ke bi.
A makon da ya gabata ma, gwamnatin Habasha ta sanar da cewa za ta bai wa motocin da ke ɗaukar kayan masarufi da kuma motocin sufurin jama’a fifiko wajen sayen mai a gidajen mai.
Recent:Jam’iyyun adawa ba su shirya karɓar mulki a hannun APC ba – Yilwatda
