Daga Mustapha Abdullahi Abubakar
Hukumar kula da babban birnin tarayya Abuja, ta amince da kwangilar sama da naira biliyan 8.4, na ayyuka masu muhimmanci da suka haɗa da kwashe shara, samar da kayan tsaro da kuma bayar da tallafi ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa.
An ɗauki matakin ne, yayin taron kwamitin zartarwa karo na 18, wanda ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya jagoranta a ranar Litinin, bayan kammala taron manema labarai.
Shugaban hukumar kula da harkokin birnin tarayya Abuja (AMMC), Feliɗ Obuah, wanda ya yi wa ƴan jarida bayanin sakamakon, ya sanar da amincewa da wasu muhimman bayanai guda biyu.
Na farko, in ji shi, wani muhimmin abu ne wanda zai taimaka wajen tsabtace yankin.
“A yau, mun gabatar da neman amincewa da wasu takardu guda biyu, waɗanda kwamitin ya amince da su.
Ya ƙara da cewa, bayani na biyu, wanda kuma ya samu amincewar kwamitin shi ne, “neman amincewa da bayar da kwangilar sayan kayan abinci, domin tallafa wa waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a FCT.”
A wani gagarumin yunƙuri na ƙarfafa gine-ginen tsaro na babban birnin ƙasar, kwamitin ya kuma amince da sayo kayayyakin sadarwa na hukumar tsaro na babban birnin tarayya Abuja.
Musa Idris Onsachi, Daraktan kula da sayan kayayyaki na babban birnin tarayya, ya bayar da cikakken bayani a kan wannan amincewa, inda ya danganta ta kai tsaye da umarnin da ministan babban birnin tarayya ya bayar.
Recent:Bauchi Launches SightQuest Programme To Combat Preventable Blindness
