Daga Mustapha Abdullahi
Hukumar National Youth Service Corps (NYSC) ta sanar da cewa za ta buɗe shafinta na yanar gizo domin matasa masu shirin yin bautar ƙasa su yi rajista na tura su aiki (mobilisation) daga 12 zuwa 18 ga Maris, 2026.
Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wani sanarwa da ta wallafa a shafukanta na sada zumunta a ranar Juma’a.
A cikin sanarwar da aka aika wa matasan da ake sa ran za su yi bautar ƙasa, hukumar ta ce ɗaliban da sunayensu kawai suka bayyana a jerin da Majalisar Jami’a (Senate) ko Hukumar Ilimi ta makaranta ta amince da su, kuma makarantu sun tura bayanansu zuwa shafin NYSC, su ne kawai za su iya yin rajista.
Ta ƙara da cewa waɗanda suka cancanci yin rajista su ne:
Hukumar ta kuma shawarci matasan da su ziyarci shafin yanar gizon NYSC da shafukanta na sada zumunta domin samun cikakkun bayanai kan yadda ake yin rajistar.
Haka kuma ta jaddada muhimmancin tabbatar da sahihancin bayanan mutum kafin fara rajistar.
A cewar hukumar, dole ne matasan da za su yi bautar ƙasa su tabbatar cewa sunansu a bayanan Hukumar NIMC (National Identity Management Commission) ya yi daidai da sunan da ke cikin jerin Senate da kuma shafin NYSC.
An kuma shawarci waɗanda suka kammala karatu su tabbatar cewa sunayensu sun yi daidai da waɗanda ke kan takardun shaidar karatunsu ko sakamakonsu
NYSC ta kuma umurci masu neman yin rajistar da su fara tabbatar da bayanansu ta hanyar shafin duba jerin Senate, kafin su ci gaba da rajistar ta yanar gizo.
Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ake aiwatar da sabbin gyare-gyare a bangaren ilimi, domin ƙarfafa sahihancin bayanan karatu.
Karanta:Bauchi Assembly Committee Reviews Katagum LGA N12.44bn 2026 Budget Plan
Ministan Ilimi, Maruf Tunji Alausa, ya sanar da cewa gwamnati za ta ɗauki tsauraran matakai domin dakile magudin takardun shaidar karatu, inda ya gargadi cewa duk wanda ba shi da sahihan takardu ba zai samu damar shiga shirin NYSC ba.
Alausa ya ce Gwamnatin Tarayya na ƙarfafa tsarin bin dokokin makarantu da kuma kula da bayanan karatu, a wani ɓangare na gyare-gyaren da ake yi domin kare martabar tsarin ilimin ƙasar nan.
Ministan ya bayyana hakan ne a yayin wani shirin horaswa na ƙasa da aka shirya domin tallafa wa aiwatar da Nigeria Education Repository and Data Bank.
Recent:Dambam LGA Defends N8.5BN 2026 Budget Before Bauchi Assembly Committee
