Daga Mustapha Abdullahi
Uwargidan shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu, za ta gabatar da wa’azi a fadar Lambeth a ranar Alhamis, a matsayin wani ɓangare na ziyarar aiki da mijinta, Bola Ahmed Tinubu, ke yi a ƙasar Birtaniya .
Wannan ita ce ziyarar farko ta shugaban Najeriya zuwa Birtaniya cikin shekaru 37, kuma wa’azin da Oluremi za ta yi ya zama tarihi, domin babu wani ɗan Najeriya da aka taɓa sani ya yi wa’azi a wannan wuri.
Za ta yi wa’azin ne a ƙarƙashin jagorancin Sarah Mullally, wacce ita ce mace ta farko da ke riƙe da wannan muƙami. Ana sa ran wa’azin zai mayar da hankali kan gaskiya, shugabanci da kuma muhimmancin ɗabi’u wajen gina ƙasa.
Oluremi Tinubu, wacce aka naɗa fasto a Redeemed Christian Church of God a 2018, ta ƙara yawan halartar tarukan addini a baya-bayan nan, ciki har da taron addu’a na ƙasa da aka yi a Washington DC.
A yayin ziyarar, Shugaba Tinubu zai gana da Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, da sauran jami’ai da ‘yan kasuwa domin tattauna batutuwan haɗin gwiwa.
Tun da fari, Sarki Charles III da Sarauniya Camilla sun karɓi shugaban ƙasar da mai dakinsa a Windsor Castle, inda aka yi musu tarba ta musamman tare da harba bindigogi 42 na girmamawa.
Ana sa ran za a gudanar da liyafar ƙasa inda shugabannin biyu za su gabatar da jawabai.
Recent:NAFDAC ta gargadi ‘yan Najeriya kan yaduwar jabun magungunan cutar kansa
