Dakarun Hukumar Kwastam ta Ƙasa (NCS), reshen ayyuka na musamman, FOU Zone C da ke Owerri, ta kama ƙwayar tramadol da sauran miyagun ƙwayoyi da darajarsu ta kai kimanin Naira biliyan 1.05 a kan babbar hanyar Okada/Ofosu da ke Benin, jihar Edo.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka fitar ga manema labarai a jiya Asabar.
Kwanturolan yankin, Comptroller Bishir Balogun, ya ce an samu nasarar kama kayayyakin ne sakamakon samun bayanan sirri da kuma haɗin gwiwar jami’an tsaro.
Ya bayyana cewa jami’an Kwastam sun tare wata mota dauke da kayayyakin da ake zargin haramtattu ne, inda direban ya yi kokarin tserewa bayan an tare shi, amma daga bisani ya bar motar ya gudu cikin daji.
Karanta:Ya kamata a zage dantse wajen kare haƙƙin ɗan adam a Afirka – Anukam
Balogun ya ƙara da cewa binciken da aka yi wa motar ya nuna cewa an boye magungunan a cikin wasu halastattun kaya don yin basaja.
Ya gargadi masu safarar kayayyakin haramtattu da su daina irin waɗannan ayyuka, yana mai jaddada cewa hukumar za ta ci gaba da amfani da dabarun leken asiri wajen kare lafiyar al’umma da tsaron ƙasa.
Ya kuma bayyana cewa kayayyakin da aka kama suna hannun hukumar, yayin da ake ci gaba da bincike domin gano wadanda ke da hannu a safarar.
Recent:Dalilan da su ka sanya ba mu cimma matsayar tsagaita wuta ba – Iran.
