Daga Mustapha Abdullahi
Bikin rajistar, wanda ya gudana a babban zauren taro mai kujeru 500 na kwalejin, ya tabbatar da shigar ɗaliban cikin shirye-shiryen karatu daban-daban na makarantar, tare da zama matakin farko na fara tafiyar karatunsu.

Taron ya samu halartar shugabannin makaranta, manyan jami’ai, ma’aikata, iyaye da sauran masu fatan alheri, waɗanda suka taru domin shaida wannan muhimmin biki.
A cikin jawabinsa, shugaban kwalejin (Rector), Dakta Hashim Sabo Bello (Sarkin Dinawan Dass na farko), ya taya sabbin ɗaliban murna, tare da ƙarfafa musu gwiwa su kasance masu mai da hankali, ladabi da jajircewa a karatunsu.
Recent:Wajibi dakarun Nijeriya su rika musayar bayanan sirri – Ministan Tsaro.
Ya kuma jaddada muhimmancin bin dokoki da ƙa’idojin makaranta yadda ya kamata, tare da ƙarfafa su su riƙa kyawawan halaye a tsawon zamansu a kwalejin.
Haka kuma, shugaban ya tabbatar wa ɗaliban cewa shugabancin makarantar na ci gaba da ƙoƙarin samar da ingantaccen yanayin karatu da ilimi mai inganci, wanda zai basu ƙwarewar da ake buƙata domin ci gaban ƙasa.
Muhimmin ɓangare na bikin shi ne rantsar da ɗaliban, wanda ke nuna amincewarsu da shiga cikin al’ummar ilimi ta Kwalejin Fasaha ta Abubakar Tatari Ali a hukumance.
Kwalejin ta yi wa ɗaliban fatan alheri tare da nasara a tafiyar karatunsu.
Recent:An kashe Birgediya Janar Oseni Braimah a harin Boko Haram a Borno.
