Daga Sani Adamu Hassan
Kotun daukaka kara da ke Abuja ta tabbatar da hukuncin da ya hana Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabijin ta Nijeriya (NBC) kakaba tara ga kafafen yada labarai a fadin kasar.
Kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito, Mai shari’a Oyebiola Oyewumi ta bayyana hukuncin a madadin kwamitin alkalai uku, inda kotun ta yi watsi da karar da NBC ta shigar domin kalubalantar hukuncin kotun tarayya.
karanta:COAS Ya Jagoranci Tawagar Tsaro Zuwa Filato, Ya Yi Alkawarin Samar da Zaman Lafiya Mai Dorewa
Kotun ta kuma soke tarar da NBC ta kakaba wa gidajen rediyo da talabijin 45 a ranar 1 ga Maris, 2019, bisa zargin karya dokokin yada labarai na kasa.
Kwamitin alkalan, karkashin jagorancin Mai shari’a Abba Mohammed tare da Mai shari’a Donatus Okorowo, ya ce hukuncin kotun baya yana nan daram, don haka NBC ba ta da ikon kakaba irin wannan tarar.
Recent:Bankin Duniya ya amince da rancen dala miliyan 500 domin tallafa wa ƙananan manoma a Najeriya.
