Daga Mustpha Abdullahi
Mataye da ‘yan uwan wasu jami’an soja da ake tsare da su bisa zargin shirya juyin mulki sun roƙi Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, da ya ba su damar ganin mazajensu tare da tabbatar da cewa ko dai a sake su ko kuma a gurfanar da su a gaban kotu.
An bayyana wannan roƙo ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Juma’a, inda iyalan waɗannan jami’ai tare da lauyan kare haƙƙin bil’adama, Deji Adeyanju, da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Omoyele Sowore, suka koka cewa an tsare jami’an fiye da kwanaki 160 ba tare da an yi musu shari’a ko kuma an ba su damar yin hulɗa da iyalansu ba.
Akalla mataye 20 na waɗannan jami’an da ake tsare da su sun halarci taron tare da ‘ya’yansu, ciki har da jariri mai watanni biyu.
Daga cikin su akwai: Firdaus Usman, Farida Lawal, Hauwa Aliu, Aisha Sadiq, Hassana Salihu, Fatima Muhammad, Zahra Abba, Khadija A. Hayatu, Helen Sunday, Memuna Bashiru (wacce ta karanta jawabin), Aisha Ibrahim da jaririn watanni biyu Ahmad Musajida.
Da yake magana da manema labarai a madadin iyalan, Basir ya ce ci gaba da tsare mazajen ya jefa iyalansu cikin rashin tabbas da damuwa.Ta ce:
“Mun zo a gabanku a matsayin iyalai mataye, uwaye da ‘yan uwa waɗanda mazajensu da ‘yan’uwansu suke tsare sama da kwanaki 160 ba tare da an kai su gaban kotu a fili ba.
Fiye da watanni biyar kenan iyalanmu suna rayuwa cikin tsoro, rashin tabbas da tambayoyi marasa amsa.
“Mun zo ne yau saboda abu guda ɗaya kawai: domin mu nemi a yi adalci a fili kuma bisa tsarin kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya.
Wadannan watanni sun kasance masu matuƙar wahala ga iyalanmu.”
Ta ƙara da cewa duk da cewa an yi ta yada zarge-zarge kan jami’an a kafafen labarai, iyalansu ba su san cikakken abin da ke faruwa ba.
“Mun kalli yadda ake gabatar da labarai ga jama’a wanda ke sanya mazajenmu su fuskanci shari’a ta kafafen yaɗa labarai.
A lokaci guda kuma, wasu daga cikinmu sun fuskanci tsoratarwa daga wasu sojojin da suka rantse za su kare ‘yan Najeriya.
“Mazajenmu sun yi wa wannan ƙasa hidima cikin aminci a fagen fama, suna haɗa rayukansu cikin haɗari domin kare Tarayyar Najeriya.
Amma a yau iyalansu sun rage da tsoro, rashin tabbas da tambayoyi marasa amsa. Ba da fushi muka zo ba, sai dai da zuciya mai nauyi na mataye da uwaye,” in ji ta.
Basir ta kuma yi kira kai tsaye ga Shugaban Ƙasa da Uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu, da su shiga cikin lamarin.
Karanta:An kori mutane 22 a Jigawa sakamakon badakalar ciyarwar a watan Ramadan.
Iyalan sun ce ba su neman wata alfarma ba, sai dai a bi haƙƙin da kundin tsarin mulki ya tanada.
Muna roƙonku da ku duba dukkan gaskiyar wannan lamari mai matuƙar muhimmanci da zuciya buɗe.
“Abin da muke nema kawai shi ne abin da kundin tsarin mulkin 1999 ya ba kowane ɗan Najeriya: a ɗauki mazajenmu a matsayin marasa laifi har sai kotu mai iko ta tabbatar da laifinsu. Kada a yi amfani da zarge-zargen a matsayin wani makami ko abin ɗora laifi. Muna son a bi tsarin doka kawai — ba fiye da haka ba, ba ƙasa da haka ba.”
Lauyan da ke Abuja ya yi gargaɗi cewa a tarihin Najeriya an taɓa amfani da zargin shirya juyin mulki a kan manyan ‘yan siyasa, don haka ya roƙi hukumomi su yi taka-tsantsan wajen tafiyar da wannan lamari.
Ya kawo misali da yadda tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, aka taɓa zarginsa da shirya juyin mulki a lokacin mulkin Sani Abacha, inda aka tsare shi na tsawon lokaci duk da cewa ya musanta zargin.
Adeyanju ya kuma tuna da irin abubuwan da suka faru ga tsohon shugaban ƙasa Umaru Yar’Adua da kuma Muhammadu Buhari, waɗanda a wasu lokuta aka taɓa zarginsu da irin wannan laifi kuma aka tsare su.
Ya yi gargadin cewa waɗanda ke kan mulki a yau ma wata rana za su iya tsinci kansu a irin wannan hali, don haka ya jaddada cewa zargin cin amanar ƙasa dole ne a gudanar da shi a bayyane kuma bisa doka.
A cewarsa, gwamnati ya kamata ta gabatar da ƙwararan hujjoji a kotu kan jami’an da ake tsare da su, ko kuma a sake su idan babu wata ƙara a kansu.
Shi ma da yake magana, Sowore ya ce iyalan sun cancanci adalci da gaskiya.Ya ce:
“Ina so in ƙarfafa wa iyalan da ke cikin damuwa na waɗanda ake zargi da shirya juyin mulki cewa muna nan domin tabbatar da an yi adalci, ko da mene ne zai ɗauka.”
Ya ƙara da cewa sau da yawa ana zargin mutane da shirya juyin mulki alhali ba su da hannu a ciki.
Yayin da yake riƙe da jariri mai watanni biyu a hannunsa a taron, Sowore ya ce jaririn bai taɓa ganin mahaifinsa ba tun bayan haihuwarsa.
Sowore ya jaddada cewa ko da zargin gaskiya ne, dole ne a yi wa waɗanda ake zargin shari’a cikin adalci da a bayyane.
Karanta:INEC ta karyata sanarwar dake cewa masu rike da mukmai su yi murabus don shiga zaɓen 2027
“Bai kamata mu zauna a ƙasa mai mulkin dimokuraɗiyya inda ake yin abubuwa a ɓoye ba. Ko da gaskiya ne cewa waɗannan mutane sun aikata laifin, suna da haƙƙin a yi musu shari’a a fili, cikin gaskiya da adalci a gaban kotu.”
Recent:Mazauna Bauchi Sun Koka Kan Wahalar Da Suka Sha Bayan Harin ‘Yan Bindiga
