Babban Hafsan Sojin Ƙasa (COAS), Laftanar Janar Waidi Shaibu, a ranar Alhamis ya jagoranci wata babbar tawagar duba harkokin tsaro zuwa Jihar Filato, inda ya sake jaddada ƙudirin rundunar sojin Najeriya na dawo da zaman lafiya da tabbatar da kwanciyar hankali mai ɗorewa a yankin.
Da isarsa Jos, COAS ya samu tarba daga Gwamnan Jihar Filato, , lamarin da ke nuna kyakkyawar haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da rundunar soji wajen magance matsalolin tsaro.
Haka kuma, ya karɓi cikakken bayani daga Manjo Janar Folusho Oyinlola, Babban Kwamandan Runduna ta 3 da kuma Kwamandan Joint Task Force Operation ENDURING PEACE, kan yadda ake gudanar da ayyukan tsaro da matakan da ake ɗauka domin dakile barazana da daidaita yankunan da abin ya shafa.
Karanta:Kwankwasiyya ta soki Tinubu kan ciyo bashin dala biliyan 6
COAS ya kuma gana da shugabannin al’umma da mazauna yankin, inda ya basu tabbacin cewa rundunar sojin Najeriya za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma masu bin doka.
Ya buƙaci jama’a da su kwantar da hankalinsu, su kasance masu lura da tsaro, tare da bai wa jami’an tsaro haɗin kai, ciki har da bin dokar hana fita (curfew) da ake ciki.
Ziyarar ta samu karɓuwa daga jami’an ƙananan hukumomi, inda Shugaban Ƙaramar Hukumar Jos North, Hon. Barr. John Kyoroh Christopher, ya yaba da wannan mataki, yana mai cewa zuwan babban hafsan sojin zai ƙara wa jama’a kwarin gwiwa da kuma ƙarfafa amincewa da matakan tsaron da ake ɗauka.
Rundunar Sojin Najeriya ƙarƙashin jagorancin Laftanar Janar Waidi Shaibu na ci gaba da jajircewa wajen aiki tare da sauran hukumomin tsaro, Gwamnatin Jihar Filato da sauran masu ruwa da tsaki domin magance matsalolin tsaro da dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a jihar.
Recent:Jam’iyyar ADC ta zargi APC da amfani da INEC domin haddasa rikici bayan shigar Kwankwaso
