Daga Mustapha Abdullahi Abubakar
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi Allah-wadai da kakkausar murya kan kashe-kashen da kuma sace fiye da mutane 100 da aka yi, lokacin da wasu da ake zargin ‘yan ta’addar Boko Haram/ISWAP suka kai hari a ƙauyen Ngoshe da ke ƙaramar hukumar Gwoza a jihar Borno.
Atiku ya bayyana wannan Allah-wadai ne a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook wanda aka tabbatar da ingancinsa, a ranar Juma’a.
Ya ce:“Harin da wasu da ake zargin ‘yan ta’adda suka kai kan sansanin sojoji da kuma sansanin ‘yan gudun hijira (IDP) a Ngoshe, ƙaramar hukumar Gwoza ta jihar Borno, wanda ya kai ga sace fiye da mutane 100, lamari ne mai matuƙar tayar da hankali.”
Ya ƙara da cewa:“Abin da ya fi tayar da hankali shi ne yadda gwamnatin tarayya ta nuna kamar ba ta damu da wannan lamari ba, da kuma irin hare-haren da suka gabata makamancin haka.”
Ya ci gaba da cewa tashin hankalin da kashe-kashe a ƙasar sun ƙaru sosai har ta kai ga gwamnati da al’umma suna nuna kamar sun saba da zubar da jini sakamakon irin waɗannan hare-hare.
Atiku ya ce abin takaici ne yadda gwamnatin tarayya ta yanzu ke nuna kamar tana rasa ƙarfi wajen yaƙar ta’addanci da hare-haren tashin hankali.
Ya ƙara da cewa maimakon mayar da hankali kan tsaro, gwamnatin tana fi mayar da hankali wajen matsa lamba ga ‘yan adawa a siyasa da kuma ƙarfafa wasu ƙungiyoyin kabilanci masu neman biyan bukatun kansu.
Karanta:CIKAKKEN JERIN SUNAYE: Jakadu 65 da Bola Ahmed Tinubu ya nada da kasashen da za su je
Ya kuma bayyana cewa abin baƙin ciki ne yadda masu kula da harkokin tsaron cikin gida tare da manyan jam’iyyar da ke mulki suka fi maida hankali kan ƙarfafa mulkinsu, alhali kuwa fararen hula da jami’an tsaro ke ci gaba da rasa rayukansu.
“Atiku ya ce yana jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a harin Ngoshe, amma dole ne ya nuna matuƙar ɓacin ransa kan yadda gwamnati ta nuna rashin tausayi ga waɗanda abin ya shafa, duk da yawaitar irin waɗannan hare-hare.”
INEC ta karyata sanarwar dake cewa masu rike da mukmai su yi murabus don shiga zaɓen 2027
Atiku, wanda jigo ne a jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), ya yi kira da a ɗauki matakan gaggawa domin magance matsalar tsaro a ƙasar.
