Daga Mustapha Abdullahi Abubakar
Gwamnatin Jihar Jigawa State ta kori masu sayar da abinci da wasu kamfanoni guda 22 da ke cikin shirin bude-baki na watan Ramadan da ake gudanarwa, sakamakon zargin yaudara, rashin gaskiya kan ingancin abinci da yawansa, da kuma wasu mu’amalolin kudi da ake zargi da rashin gaskiya.
An dauki wannan mataki ne domin tabbatar da gaskiya da rikon amana a cikin shirin da aka kirkira domin ciyar da marasa karfi a cikin watan Ramadan mai alfarma
shirin, wanda yake da nufin tallafa wa mutane miliyan 7.9 ta hanyar cibiyoyin rabon abinci kyauta guda 640 a fadin jihar, gwamnan jihar Umar Namadi ne ya kaddamar da shi domin taimaka wa talakawa da samar musu da abinci mai gina jiki a Ramadan na shekarar 2026.
Sai dai bayan kusan mako biyu kacal da fara shirin, wani cikakken rahoton sa ido da binciken da aka gudanar a wuraren rabon abinci ya bankado manyan laifuka da rashin gaskiya daga wasu masu sayar da abinci da kamfanoni, bayan koke-koken da jama’a suka yi.
Wannan lamari ya sa Ma’aikatar Harkokin Jin Kai da Ayyuka na Musamman ta jihar ta dauki mataki cikin gaggawa, inda ta kori wadanda ake zargi da hannu a cikin badakalar.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Harkokin Jin Kai da Ayyuka na Musamman na jihar, Auwalu Sankara, ya fitar ga manema labarai a birnin Dutse a ranar Juma’a, ya ce an kori mutanen ne saboda mummunar dabi’a a aiki, almundahana da kudaden gwamnati, da kuma rashin kula da shirin yadda ya kamata.
Sanarwar ta bayyana sunayen wadanda abin ya shafa kamar haka:
Haruna Ladan Inv. and Property (Jahun LGA)
Musa A. Jibrin (Gwiwa 1, Jahun LGA)
Nura Yahaya (Chukuto Ward, Taura LGA)
Usman Umar Malam (Sarawa 1, Kafin Hausa LGA)
Muhammad Suleiman (Sarawa 2, Kafin Hausa LGA)
Musa Salisu (Zago 1, Kafin Hausa LGA)
Dauda Yusuf (Zago 2, Kafin Hausa LGA)
Lurwanu Alhassan (Unguwar Ya 1, Birnin Kudu LGA)
Ashiru Kamisu (Danladi 1, Sule Tankarkar LGA)
Shuaibu Muhammad (Danladi 2, Sule Tankarkar LGA)
Muhammad Abdullahi (Jeke 1, Sule Tankarkar LGA)
Jafaru Magaji (Amanga 1, Sule Tankarkar LGA)
Sauran sun hada da:
Sulaiman Shuaibu (Yayari 1, Hadejia LGA)
Badamasi Umar (Yayari 2, Hadejia LGA)
Danbaba Nasallah (Matsaro 1, Hadejia LGA)
Fatima Abdulaziz (Yankoli 1, Hadejia LGA)
Ibrahim Sulaiman (Yankoli 2, Hadejia LGA)
Yusuf Wada (Jahun)
Haruna Yau da Aisha Garba (Malam Madori)
Babannan Baffa (Guri)
Amina Abdullahi (Gwaram)
Kwamishinan ya ce:
“An kori wadannan mutane da kamfanoni ne saboda mummunar dabi’ar aiki, almundahana da kudaden jama’a, da kuma rashin gudanar da shirin yadda ya kamata.”
Ya kara da cewa gwamnatin jihar tana da manufar rashin jurewa duk wani aiki da zai lalata manufar taimakon jama’a da gwamnatin gwamna Umar Namadi ta kafa.
Recent:Wike Ya Amince Da Kashe Naira Biliyan 8.4 Domin Shawo Kan Matsalar Tsaro A Abuja
