Wani jirgin yakin Sojojin saman Nigeria ya sake kashe fararen hula da dama a matsugunan Guradnayi da ke gab da garin Kasasu a Karamar hukumar Shiroro ta jihar Niger
Majiyoyi sun bayyana cewa, lamarin ya faru ne da sanyin safiyar yau Lahadi inda bayanai ke cewa wasu iyalan gabaki daya suka rasa rayukansu a wannan hari, yayinda kusan dukkanin gidajen da ke Guradnayi suka rasa akalla mutum guda zuwa sama daga cikin iyalansu
karanta:Red Cross ta yi gwajin cututtuka da bada magunguna kyauta ga mutane 1,500 a Kano
Wani mazaunin Kusasu Auta Awododo ya shaida cewa da misalin karfe 5 na asubahin yau Lahadi aka kai harin, yace a gidan wani dan uwansa kadai mutane 12 suka mutu sanadiyyar harin sojojin Nigeria
A cewar Awododo galibin wadanda harin Sojojin ya rutsa da su mutane ne da suka tserewa hare-haren ‘yan ta’adda a Kusasu
Wata majiya ta daban tace harin Sojin saman Nigeria ya faru ne bayan wucewar ayarin ‘yan bindiga haye akan babura ta cikin kauyukan da ke gab da Kusasu wadanda sojoji ke biye da su, kamar yadda RFI suka ruwaito
Recent:Amb Yusuf Maitama Tuggar: Miles Away From An Underachiever
