<strong>Hukumar kula da yanayi ta Najeriya Nimet ta yi gargaɗi cewa akwai yiwuwar jihohi 18 a ƙasar su fuskanci ambaliya cikin kwanaki masu zuwa sakamakon ruwa kamar da bakin ƙwarya da ake tsammanin yi.
A wata sanarwar gargaɗi da ta wallafa a shafinta na X jiya Alhamis, Nimet ta ce jihohin da ka iya fuskantar ambaliyar sun haɗa da Zamfara da Nassarawa da Kwara da Oyo da Legas da Ogun da Ekiti da Delta da Imo da Anambra da Enugu da Ebonyi da Akwa Ibom da Cross River da Rivers da Edo da Ondo da Bayelsa.
A cewar hukumar, ambaliyar na iya janyo tsaiko wajen wucewar motoci da yin ɓarna ga wasu gidaje da gonaki da gine-gine sai toshewar magudanan ruwa da rashin lantarki da matsalar sadarwa da kuma haɗurran yaɗuwar cututtuka.
Karanta:Masu neman takarar gwamnan Yobe a APC sun yi watsi da tsayar da ɗan takara ta maslaha
Nimet ta kuma shawarci jama’a da ke jihohin da su ɗauki matakan da suka dace ta hanyar tsaftace magudanan ruwan da ke gidajensu sannan kuma su riƙa duba hasashen yanayi a kai a kai.
Hukumar ta gargaɗi masu ababen hawa da masu tafiya a ƙafa da su kaucewa yin tuƙi ko ma bi ta wuraren da ambaliya ta mamaye.
Gargaɗin na zuwa ne bayan da gwamnatin ƙasar ta yi gargaɗi cewa wasu jihohi 33 har da birnin tarayya Abuja na cikin haɗarin fuskantar ambaliya a 2026.
