Daga Mustapha Abdullahi Abubakar
wani lamari mai Tashin hankali ya sake karuwa a kauyen Gero da ke karamar hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato, bayan da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kashe masu hakar ma’adinai uku a daren Juma’a, yayin da suke kan hanyarsu ta dawowa daga aiki.
Lamarin ya kara jefa tsoro da fargaba a zukatan al’ummar yankin, musamman ganin cewa kwanaki kadan da suka gabata ne aka kashe wani makiyayi Bafullatani mai suna Shafiu Idris, mai shekaru 30.
Rahotanni sun ce an kai masa hari ne a ranar Laraba yayin da yake dawowa daga kiwon shanunsa a wannan kauye na Gero, kamar yadda shugaban kungiyar Miyetti Allah a Jos ta Kudu, Alhaji Ahmad Mu’azu ya bayyana.
Karanta:Ƴan ta’adda sun sace sama da mutane 150 a Zamfara
Dangane da haka, an bukaci hukumomin tsaro da su dauki matakan gaggawa tare da tsaurara tsaro domin dakile yaduwar rikici da kuma dawo da zaman lafiya a yankin. Haka kuma, an nemi a gudanar da cikakken bincike domin gano wadanda suka aikata wannan aika-aika tare da gurfanar da su a gaban kuliya.
A halin yanzu, mazauna yankin na ci gaba da kasancewa cikin fargaba, yayin da ake kara kira ga zaman lafiya da kuma bukatar karin jami’an tsaro a yankin.
