Daga Mustapha Abdullahi
Shirin tallafawa manoma na Special Agro-Industrial Processing Zones (SAPZ) na ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa harkar noma a jihar Kano, ta hanyar samar da tallafin Matching Grant domin kara yawan amfanin gona da inganta samar da abinci.
Babban sakataren na ma’aikatar Noma da albarkatun kasa ta Kano, Alhaji Bashir Sanusi, ya bayyana cewa shirin na bai wa manoma, kungiyoyi da ‘yan kasuwar noma damar fadada ayyukansu da kuma kara karfin gogayya da sauran Manoma a kasuwa.
Ya jaddada cewa an samar da tsarin sa ido na na wani daga wajen shirin domin tabbatar da gaskiya, rikon amana da kuma ingantaccen aiwatar da shirin, musamman wajen tabbatar da cewa tallafi ya kai ga wadanda suka dace.
Ya bayyana hakan ne a yayin taron masu ruwa da tsaki kan shirin Matching grant da aka gudanar a Kano a ranar Alhamis.
Karanta:Uba ya fasa aurar da ƴarsa ga wani masoyin shugaba Tinubu a Jigawa
Shi ma Mai Kula da Shirin SAPZ a Kano, Aminu A. Iliyyasu, ya ce shirin wani babban tsari ne na gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar cibiyoyin kasa da kasa, wanda ke da nufin bunkasa noma, karfafa samar da abinci da kuma kara fitar da kayayyaki waje.
Ya kara da cewa shirin zai amfanar da mutane kusan 100,000 a jihohin Kano da Ogun, inda aka ware kaso 50% ga mata da 40% ga matasa.
A karshe, ya bukaci masu ruwa da tsaki da su bayar da hadin kai domin tabbatar da nasarar shirin da cimma manufofinsa.
