Daga Mustapha Abdullahi Abubakar
Rundunar ‘yan sandan Jihar Jigawa ta nuna tausayi ga zawarawa 100 na jami’an da suka rasu, inda ta raba musu kayan abinci a wani shiri na jin-kai domin tunawa da Ranar Mata ta Duniya a ranar Laraba.
Wakilin jaridar The PUNCH ya ruwaito cewa an gudanar da taron ne a Hedikwatar Rundunar ‘yan sandan jihar, domin girmama sadaukarwar mata tare da tallafa wa iyalan ‘yan sanda.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, CP Dahiru Muhammad, ne ya jagoranci shirin ta hannun mataimakinsa, DCP Tijjani Murtala.
Da yake jawabi a wurin taron, DCP Murtala ya yi magana kan muhimmancin Ranar Mata ta Duniya, yana mai jaddada jajircewa da nasarorin da mata ke samu Ya ce:
“Mata suna taka muhimmiyar rawa a matsayin jami’ai, uwaye, matan aure da kuma masu kula da iyali.”
Ya bayyana cewa wannan shiri an yi shi ne domin tallafa wa zawarawan jami’an da suka rasa rayukansu yayin hidima, wanda hakan ke nuna kudirin rundunar wajen girmama sadaukarwar su.
Yayin da yake mikawa zawarawan kyaututtukan da kansa, DCP Murtala ya ce yana fatan wannan tallafin zai sa murmushi a fuskokin matan jaruman da suka sadaukar da rayuwarsu.
Har ila yau ya jaddada cewa:
“Dole ne mu ci gaba da tallafa wa juna, musamman iyalan jarumanmu da suka rasu.”
Ya kara da cewa mata suna da muhimmiyar rawa a aikin ‘yan sanda da kuma cikin al’umma gaba daya, yana cewa:
“Mata su ne ginshikin al’umma, kuma wajibi ne mu tallafa musu.”
Ya kuma bayyana cewa jagorancin CP Dahiru Muhammad yana bai wa iyalan jami’an da suka rasu muhimmanci, tare da tabbatar da cewa sadaukarwar su ba za ta tafi a banza ba.
Tun da farko a jawabinta, Mrs. Dinna Yunana, wadda ta wakilci shugabar POWA, ta yaba da wannan shiri na rundunar, tana mai jaddada kudirin kungiyar na kula da jin dadin iyalan ‘yan sanda.Ta ce:
“Muna godiya da kokarin rundunar wajen tallafa wa iyalanmu.”
Ta kara da cewa taron ya nuna yadda rundunar ke da kuduri wajen kula da jin dadin jama’a, tausayi da hadin kai a cikin iyalan ‘yan sanda.
“POWA na ci gaba da tallafa wa iyalan ‘yan sanda tare da karfafa hadin kai. Za mu ci gaba da aiki tare da rundunar domin tabbatar da cewa iyalanmu sun samu tallafin da suke bukata,” in ji ta.
Ta kuma bayyana cewa taron ya girmama nasarori da sadaukarwar mata, tare da nuna karfinsu da jajircewarsu.
Wakilin The PUNCH ya ruwaito cewa kayan abincin da aka raba wa iyalai 100 na jami’an da suka rasu a rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa sun hada da buhunan shinkafa da kwandunan taliya (spaghetti).
Wasu daga cikin wadanda suka amfana sun nuna godiyarsu bayan karbar kayan.
Wata daga cikinsu, Aisha Yakubu, ta ce:
“Muna godiya ga rundunar da ta tuna da mu tare da tallafa mana. Wannan taimako zai kara mana karfin gwiwa mu ci gaba da tallafa wa iyalan jarumanmu da suka rasu.”
Ita ma wata matar jami’in dan sanda da ya rasu, Maryam Idris, ta ce:
“Wannan tallafi ya kawo mana farin ciki da fata. Muna matukar godiya da alherin da rundunar ta nuna mana.”
Recent:CG AUDI YA INGANTA DOKAR TSARON DAN ADAM A AIKIN NSCDC
