Daga Zenith Media™
Kungiyar kare hakkin Musulmi ta Muslim Rights Concern (MURIC) ta yi tir da Allah wadai da abin da ta bayyana a matsayin ci gaba da tsare tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta bukaci hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta gurfanar da El-Rufai a gaban kotu idan akwai tuhume-tuhume a kansa, ko kuma su sallame shi idan ba a shirya gabatar da shi gaban shari’a ba.
MURIC ta jaddada cewa bin ka’idojin doka da mutunta hakkin dan Adam su ne ginshikin dimokuradiyya, tare da kira ga hukumomi da su tabbatar da gaskiya da adalci a duk wani mataki da za su dauka.
Kungiyar ta kuma bayyana fatan cewa matakin da za a dauka zai kasance cikin bin doka da oda, domin kare martabar kasa da kuma tabbatar da zaman lafiya.
Zenith Media™ na ci gaba da bibiyar karin bayani kan lamarin.
Zaku iyaka karanta wannan:Har yanzu El-Rufai na hannun EFCC, A hannun EFCC El-Rufai ya kwana
