Mai bai wa tsohon gwamnan Kaduna, Nasiru El-Rufai shawara kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ya bayyana cewa har yanzu El-Rufai yana hannun EFCC.
Adekeye ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X inda ya ce El-Rufai ya amsa gayyatar da hukumar ta aika masa a jiya Litinin, inda ya je ya amsa tambayoyi kamar yadda aka buƙace shi.
Ya ƙara da cewa “ganawar da aka yi tsakanin El-Rufai da jami’an hukumar ta kasance mai amfani kuma cikin fahimta.
A cewarsa, “lauyan tsohon gwamnan ya lura cewa jami’an da suka karɓe shi sun nuna ƙwarewa da mutunci wajen gudanar da aikinsu”
Sanarwar ta kuma bayyana cewa har yanzu tsohon gwamnan yana tare da jami’an hukumar, ba tare da bayyana ko yaushe za a sallame shi ba, ko kuma ko an kammala tambayoyin da ake masa ba.
Hukumar EFCC dai ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan batun ba zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
El-Rufai dai wanda ke cikin jagororin adawa a ADC da ke shirin ƙalubalantar shugaban ƙasa Bola Tinubu na APC a zaɓe mai zuwa, ya zargi gwamnati da matsa wa ‘yan adawa lamba ta hanyar binciken rashawa. Ya kuma ce an riga an kama kusan mutane huɗu da suka yi aiki tare da shi a Kaduna, yana mai cewa yana ganin lokaci ne kawai kafin a gayyace shi, abin da yanzu ya tabbata.
