Daga Mustapha Abdullahi
Ƙungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya (ASUU), reshen Jami’ar Jos (UniJos), ta sanar da shiga yajin aikin sai baba-ta-gani sakamakon jinkirin biyan albashin watan Maris na 2026 da kuma rashin saka alawus-alawus.
Shugaban reshen ƙungiyar, Farfesa Jurbe Joseph Molwus, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, inda ya ce yajin aikin zai fara aiki nan take daga ranar 8 ga Afrilu, 2026.
A cewarsa, bayan bin dukkan matakan da suka dace, an umarci dukkan mambobin ƙungiyar da su dakatar da koyarwa, gudanar da jarabawa da kuma halartar tarukan aiki har sai an biya su haƙƙoƙinsu.
Karanta:PowerShift Project Trains Youth Leaders On Digital Rights, Civic Tech In Jos
“Mun nuna haƙuri sosai amma har yanzu ba a biya albashin watan Maris ba. Saboda haka, muna kira ga dukkan mambobi su dakatar da duk wani aiki har sai an biya mu,” in ji shi.
Molwus ya danganta jinkirin biyan albashin da ofishin Akanta Janar na Tarayya, yana mai cewa sashen kuɗi na jami’ar ya kammala nasa ɓangaren a tsarin biyan albashin.
Recent:Kaduna Group Blasts ADC Faction Over ‘Kangaroo’ Press Conference, Carpets Maina
